in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cibiyar bada ceto ta Indonesia ta ce an gano jelar jirgin saman "AirAsia"
2015-01-07 16:50:44 cri
Shugaban cibiyar bada ceto ta kasar Indonesia ya bayyana a gun taron manema labaru a ranar 7 ga wata cewa, ma'aikatan aikin bada ceto sun gano jelar jirgin saman kamfanin "AirAsia" da ya fadi ta hanyar daukar hotuna a karkashin teku.

A ranar 7 ga wata, an shiga kwana na 11 wajen neman tarkacen jirgin saman na kamfanin "AirAsia" da ya fadi. Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Reuters ya bayar, an ce, shugaban kula da aikin neman jirgin saman na kasar Indonesia ya tabbatar da cewa, an gano jelar jirgin saman a tekun Java, kana ya tabbatar da hotunan da aka dauka, domin jelar da aka gano tana dauke da kalmomin "AirAsia" (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China