Yayin taron na jiya Talata wakilan ofisoshin jakadancin kasashen Afirka kamar Madagascar, da Habasha, da Uganda, da Kamaru, da Guinea, da Cote d'Ivoire da sauransu dake nan kasar Sin, sun tattauna tare da 'yan kasuwar kasar Sin kimanin 100 kan harkokin zuba jari a kasashen Afirka.
Wakilai daga ofisoshin jakadancin kasashen Afirkan sun gabatar da bayanai, kan manufofin zuba jari na kasashensu, da ayyukan jawo jari daga ketare.
Jakada mai kula da harkokin ciniki na kasar Habasha dake Sin Abebe Tadesse Duressa ya bayyana cewa, zuwa jarin Sin a kasashen Afirka kai tsaye, na da nasaba da raya masana'antu a nahiyar, kana zai taimaka wajen daga darajar hajojin Afirka, da kuma gabatar da sabbin fasahohi ga Afirka.
'Yan kasuwar kasar Sin din dai na nuna sha'awa kwarai ga zuba jari a kasashen Afirka. A nasa bangare shugaban cibiyar nazarin tattalin arzikin Sin da kasashen Afirka Yang Zhongqiang ya bayyana cewa, bunkasuwar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a fannonin tattalin arziki da cinikayya, na sa kaimi ga kyautata zamantakewar jama'a da tattalin arziki a kasashen Afirka, kana ta nuna goyon baya ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin.
Ya zuwa yanzu kamfanoni fiye da dubu 2 ne suka zuba jari, suke kuma gudanar da huldodin kasuwanci a kasashen Afirka, musamman a fannonin gine-gine, da hada-hadar kudi, da kere-kere, da hakar ma'adinai, da sadarwa, da aikin gona da dai sauransu. (Zainab)