An bada labarin cewa, a kwanan baya, shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya bayyana cewa, Sin za ta taimaka wa kungiyar tarayyar kasashen Afirka (AU) wajen kafa rundunar sojan tinkarar matsaloli cikin gaggawa, da zummar kara karfinsu a wannan fanni.
Hong Lei ya ce, Sin ta dade ta da ba da taimako wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka. A cikin 'yan shekarun da suka wuce, Sin ta goyi baya tare da taimaka ma ayyukan kungiyar AU na a ayyukanta na kiyaye zaman lafiya a Somaliya, da Mali da sauran kasashen nahiyar bisa iyakacin kokarinta.
Ya ce, a watan Oktoban bana, Sin ta yi shawarwari da kungiyar AU kan harkar tsaro da zaman lafiya a karo na farko a karkashin tsarin yin shawarwari tsakanin Sin da kungiyar AU bisa manyan tsare tsare, inda suka yi shawarwari kan yin hadin gwiwa a fannin kafa rundunar sojan da sauransu.
Hong Lei ya kara da cewa, Sin na fatan ci gaba da goyon bayan kokarin kungiyar AU da sauran kungiyoyin shiyya-shiyya da kasashen Afirka a kokarin da su ke dasuyi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.(Fatima)