Hakan dai ya biyo bayan tayin hakan, da suka ce wasu manyan kulaflikan Turai sun yi game da sayen 'yan wasan biyu.
Da yake karin haske game da wannan batu, daraktan kulaf din na Cruzeiro Alexandre Mattos, ya tabbatar da cewa kulaf din Zenit saint Petersburg na kasar Rasha ne ya bukaci sayen Dede, kan kudi har dalar Amurka miliyan 16. Yayin da ake rade-radin cewa kulaf din Manchester United na Birtaniya ne ya nuna sha'awar sayen dan wasan gaba Ribeiro, wanda tuni hukumar kwallon kafar Brazail ta bayyana shi a matsayin daya daga 'yan wasa mafiya kwarewa a kulaflikan kasar.