in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'i mai kula da wasannin Olympics na Rio ya alkawarta gudanar gasar kan lokaci bisa kuma kasafin kudin da aka kayyade
2014-08-20 16:59:50 cri
Shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics a birnin Rio na kasar Brazil a shekarar 2016 mai zuwa Sidney Levy, ya yi alkawarin cewa za a gudanar da gasar wasannin na Olympics kan lokaci, kuma bisa kasafin kudin da aka kayyade.

Idan ba a manta ba, a baya bayan nan Brazil ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya na bana, ba tare da gamuwa da wata babbar matsala ba, duk da cewa ta gamu da tarin kalubale a kokarinta na share fagen gasar.

Hasali ma dai a yayin wancan gasa ta cin kofin duniya da aka kashewa dalar Amurka biliyan 11, kusan dukkan manyan filayen wasa 12 da aka yi amfani da su sun taba gamuwa da matsalolin neman karin kudi sama da yadda aka kayyade tun da fari, baya ga matsalar dara lokacin da aka kayyade wajen gina wadannan filaye.

Game da hakan ne ake nuna dar dar kan yanayin da 'yan wasa, da masu kallon wasa na kasashe daban daban za su iya gamuwa da shi, yayin wasannin Olympics da birnin Rio zai karbi bakunci nan da shekaru 2 masu zuwa.

Sai dai game da hakan yayin tattaunawar sa da wakilin kamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xinhua, Mr. Sidney Levy ya ce gasar Olympics din da za ta gudana a birnin Rio ba za ta gamu da matsaloli, irin wadanda gasar cin kofin duniya ta fuskanta ba, domin an riga an tsara wani shiri na gudanar da wasannin bisa sahihin kasafin kudin da ya dace.

A cewar Levy wannan kasafin kudi ya kunshi kudin da za a kashe wajen gudanar da wasanni, da kuma kudin da ake bukata domin gina filayen wasa, tare da sauran kayayyakin more rayuwar jama'a.

Har wa yau Levy ya ce yawancin kudin da ake bukata domin gudanar da gasar ta Olympics za su fito ne daga kudaden daukar nauyin gasar da na sayar da tikitin 'yan kallo, gami da gudummawar kwamitin Olympics na kasa da kasa. Kaza lika Levy ya bayyana cewa ya zuwa yanzu kudin da aka kashe ba su wuce kasafin da aka tsara ba.

Bugu da kari Mr. Levy, wanda ke kasar Sin domin halartar wasannin Olympics na matasa dake gudana a birnin Nanjing, ya yi amfani da wannan dama wajen zantawa da jami'an hukumomin wasanni kasa da kasa. Ya kuma bayyana kwarin gwiwar sa game da batun kammala gini ko gyaran filayen da za a yi amfani da su lokacin gasar ta Olympics na birnin Rio, aikin da ya ce ya zuwa yanzu ya kai kashi 55 bisa dari. Ya ce, sauran gine-ginen da suka rage ba na manyan filayen wasa ba ne.

Da aka tabo batun irin darasin da gasar ta birnin Rio za ta koya daga wasannin Olympics na matasa da ke gudana a birnin Nanjing kuwa, Levy ya ce yana fatan ganin kwatankwacin yanayin da ake da shi a birnin na Nanjing, a shekaru 2 masu zuwa lokacin da gasar za ta leka nahiyar kudancin Amurka a karon farko.

"Muna ganin kokarin da hukumomi suka yi na inganta mu'amala tsakanin mahalarta wannan gasa na da matukar muhimmanci, lallai al'umma suna jin dadin wasannin dake gudana", a kalaman Levy, wanda ya kalli wasannin ninkaya, da kwallon tebur da kuma wasan Taekwondo.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China