Murer 'yar kimanin shekaru 32 da haihuwa, wanda kuma 'yar asalin kasar ta Brazil ce, tace dukkanin 'yan kwamitin shirye-shiryen gasar Olympics din na birnin Rio, a yanzu sun maida hankula ga batun kammala tsare-tsaren wuraren da za a gudanar da gasar cin na kofin duniya, lamarinda a cewarta yasa aka yi watsi da bukatun rukunin 'yan wasan motsa jiki daban daban, da zasu halarci wasan na Olympics nan da shekaru 3 masu zuwa.
Yayin zantawarta da 'yan jaridu ranar Lahadi 25 ga watan nan, Murer ta kara da cewa, tayi tsammanin ganin canji, don gane da yanayin hali na rashin tabbas da 'yan wasa ke ciki a kasar ta Brazil, bayan kammalar wasan Olympics daya gabata a birnin Landon, amma ga alama hakan ba zai samu ba. Bugu da kari Murer na ganin shirin da ake yi na rushe filin wasa na Celio de Barros, wanda a baya yake daya daga muhimman wuraren samun horo ga 'yan wasa motsa jikin, wani nakasu ne ga 'yan wasan.
Shi dai wannan filin wasa za a rushe shine nan da 'yan makwanni masu zuwa, a shirin da ake yi na fadada filin wasa na Maracana. Murer tace ta murmure daga rashin nasarar data kwasa, bayan gaza samun lambar yabo da ta yi, yayin wasannin Olympics da suka gabata a London a shekara ta 2008, da kuma na birnin Biejing a shekarar data gabata, duk kuwa da kokarin da tayi na cimma wannan buri.(Saminu)