Simoes dan shekaru 61 da haihuwa, zai maye gurbin Vagner Mancini wanda aka sallama, bayan da kulaf din wanda a baya ya taba lashe kofin zakarun kulaflikan kasar Brazil ya fada aji na biyu, na kulaflikan kasar a farkon watan nan na Disamba.
Koci Simoes, wanda ya taba horas da kulaf din matasa na kasar Brazil, tauraruwar sa ta haska ne bayan da ya jagoranci kulaf din kasar Jamaica, zuwa gasar cin kofin duniya da aka buga a Faransa a shekarar 1998. Ya kuma taba horas da kulaflikan kasar Trinidad da Tobago, da na kasar Honduras da kulaf din mata na kasar Brazil.
Bayyana daukar Simoes din dai na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da sabon zababben shugaban kungiyar ta Botafogo Carlos Eduardo Pereira, ya ayyana sabbin manufofin tsuke bakin aljihun kulaf din, a wani yunkuri na shawo kan matsalolin bashi dake addabar kungiyar.(Saminu Alhassan)