Kafin hakan dai hukumar ta CAF ta ki amincewa da bukatar Morocco na dage lokacin gudanar gasar, kafin daga bisani a zabi kasar Equatorial Guinea a matsayin wadda za ta maye gurbin Morocco wajen daukar bakuncin gudanar gasar.
A cewar shugaban hukumar CAF Issa Hayatou, daya daga matakan da aka dauka kan Morocco shi ne, hana ta halartar gasar cin kofin na Afirka har karo biyu a nan gaba, matakin da zai haifarwa Moroccon babbar illa a fannin wasanni, musamman a matsayin ta na daya daga cikin manyan kungiyoyi dake da karfi a fannin kwallon kafar nahiyar ta Afirka. Baya ga dakatarwa, za kuma a ci tarar kasar ta Morocco kudi har dala miliyan 20.
Ya zuwa yanzu dai mutane fiye da dubu biyar ne cutar Ebola ta hallaka a wasu kasashen Afirka, wanda hakan ya sanya Morocco nuna damuwa matuka ga yiwuwar yaduwar wannan cuta a kasar ta kafar wannan gasa. Duk kuwa da cewa kasashe uku da suka fi fama da cutar ta Ebola ba za su halarci gasar a wannan karo ba.(Zainab)