141204-an-fitar-da-jerin-sunayen-yan-takarar-gwarzon-dan-kwallon-afirka-na-2014-zainab.m4a
|
'yan takarar dai sun hada da Yaya Toure wanda ake ganin mai yiwuwa ya fi sauran 'yan takarar damar cimma wannan nasara. An kuma bayyana sunayen ba tare da sanya sunan Didier Drogba na Cote d'Ivoire ba.
Bisa tsarin zaben dai daukacin masu horas da 'yan wasa na kungiyoyin kasashen Afirka za su jefa kuri'u a wannan zabe, a kuma gudanar da bikin bada lambar wanda ya samu nasara a ranar 8 ga watan Janairu na shekarar 2015 a Nijeriya.
Kafin wannan karo, Yaya Toure ya riga ya samu irin wannan yabo a shekarar 2011, da 2012 da kuma 2013, kana shi na dan wasa daya tilo daga Afirka, da ya shiga jerin sunayen 'yan wasa dake takarar gwarzon "FIFA Golden Globe Award" a wannan shekara. Hakan ne dai ya sanya shi kasancewa mafi samun damar cimma wannan nasara ta gwarzon Afirka a wannan shekara.
Baya ga Toure akwai Medhi Benatia na kasar Morocco, da Pierre Emerick Aubameyang daga Gabon, da Seydou Keita daga Mali da dai sauransu. (Zainab)