in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CECAFA ta soke gasar bana sakamakon rashin kasar da za ta dauki bakuncin ta
2014-12-23 10:01:03 cri
Gamayyar hukumar kwallon kafar Gabashi da tsakiyar Afirka ta cecafa, ta bayyana soke gasar cin kofin ta na bana, sakamakon rasa kasar da za ta dauki bakuncin gasar.

A cewar shugaban hukumar Leodegar Tenga, babban dalilin fuskantar wannan matsala ita ce tsada, ko yawan kudaden da ake bukata wajen daukar nauyin gasar.

Tenga wanda ya shaidawa manema labaru hakan bayan kammala babban taron hukumar a birnin Nairobin ranar Kenya a ranar Lahadi, ya kara da cewa dole ne Cecafan ta rage dawainiyar gasar, ta hanyar rage tsadar gudanar da ita, ta yadda hakan zai bada damar bunkasa kwallon kafa a daukacin yankin.

Ya ce koda yake CECAFA ta samu wasu kudade da suka jibanci gasar, a hannu guda kudaden ba za su isa gudanar da gasar ba.

Kasar Habasha ce dai ta janye daga daukar nauyin gasar, aka kuma rasa wata kasa ta daman da za ta maye gurbin ta, matakin da masu fashin baki ke kallo a matsayin babban koma baya ga yankin a fannin bunkasa tamaula.

Game da wannan mataki da hukumar ta CECAFA ta dauka, babban magatakardar ta Nicholas Musonye, ya ce jagororin hukumar na shirin gudanar da wani taro na musamman domin gudanar da sauye-sauyen da suka wajaba.

Musonye ya ce tun daga shekarar 1989 CECAFA ke gudanar da gasar kwallon kafa a yankin, don haka matsalar da aka huskanta a bana ba ta nufin hukumar ta gaza baki daya. A cewar sa akan bukaci kimanin dalar Amurka 600,000 wajen gudanar da gasar a wuri guda cikin makwanni 2 kacal.

Kasashen dake buga wannan gasa da CECAFAn ke shiryawa dai sun hada da Burundi, da Habasha, da Kenya, da Rwanda, da Somalia. Sauran su ne kasar Sudan ta Kudu, da Sudan, da Tanzania, da Uganda, da Zambia da kuam Zanzibar.

Kasar Kenya ce dai ke rike da kambin gasar da ta gabata a bara.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China