in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe tashar jiragen ruwa ta Es Sider a Libya sakamakon tashe-tashen hankali
2014-12-15 16:11:40 cri
Majiya daga hukumar kula da harkokin man fetur ta kasar Libya ta tabbatar a ranar 14 ga wata cewa, kungiyoyin dakaru biyu masu gaba da juna a kasar Libya sun tafka kazamin fada domin neman ikon tashar jiragen ruwa ta Es Sider da ta fi fitar da man fetur zuwa kasashen waje, lamarin da ya tilasta a rufe tashar jiragen ruwan.

Majiyar ta kara da cewa, dukkan ma'aikatan dake tashar jiragen ruwa ta Es Sider sun janye daga tashar don tabbatar da lafiyarsu.

Dakarun Fajr Libya sun kai wani samamen ba zato ba tsammani a ranar 13 ga wata da safe, a kokarin kwace tashar jiragen ruwa ta Es Sider daga hannun sojojin tsaro na Cyrenaica, (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China