in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan jarin kasashen waje da Sin ta yi amfani da shi a watan Nuwanba ya karu da kashi 22.2 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara
2014-12-16 15:55:31 cri
Kakakin ma'aikatar ciniki ta kasar Sin Shen Danyang ya bayyana a yau Talata 16 ga wata cewa, yawan jarin kasashen waje da kasar Sin ta yi amfani da shi a watan Nuwanba ya kai dala biliyan 10.36, wanda ya karu da kashi 22.2 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.

A yayin wani taron manema labaru da ma'aikatar ciniki ta kasar Sin ta shirya, mista Shen Danyang ya bayyana cewa, a watanni 11 na farkon shekarar bana, yawan sabbin kamfanonin da masu zuba jari daga kasashen waje suka kafa a kasar Sin ya kai 21296, wanda ya karu da kashi 4.2 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Yawan jarin kasashen waje da Sin ta yi amfani da shi a lokacin ya kai dala biliyan 106.24, wanda ya karu da kashi 0.7 cikin dari bisa na makamancin lokacin shekarar bara.

Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, yawan jarin kasashen waje da aka yi amfani da shi a fannin ba da hidima a kasar Sin tun daga watan Janairu zuwa Nuwanba ya kai dala biliyan 58.55, wanda ya karu da kashi 7.9 cikin dari bisa ga na shekarar bara, kana yawansa ya kai kashi 55.1 cikin dari na yawan dukkan jarin kasashen waje da Sin ta yi amfani da shi. Kana yawansa a fannin sha'anin kirkire kirkire ya kai dala biliyan 35.93, wanda ya ragu da kashi 13.3 cikin dari, kana yawansa ya kai kashi 33.8 cikin dari na yawan dukkan jarin kasashen waje da Sin ta yi amfani da shi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China