George Little ya bayyana cewa, sabo da yanayin da ake ciki yanzu a kasar Masar bai dace a tura mata wadannan jiragen saman yaki sanfurin F-16 ba, shi ya sa, kudurin da shugaba Obama ya tsayar ya samu karbuwa sosai daga dukkan masu kula da harkokin tsaron kasar. Ya kara da cewa, kasar Amurka za ta ci gaba da raya dangantakar harkokin soja da ke tsakaninta da kasar Masar, domin dangantakar ita ce tushen dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin kasashen biyu, kana tana da muhimmanci wajen kiyaye yanayin tsaron yankunan, shi ya sa ba za a soke tsarin atisayen soja da aka tsayar tsakanin kasashen biyu ba.
George Little ya kuma nuna cewa, kudurin da aka tsayar na jinkirta baiwa kasar Masar jiragen samun yakin din ba ya nufin cewa, wai Amurka tana ganin cewa an samu juyin mulki a kasar Masar sabo da rundunar sojan kasar ta hambarar da Mohamed Morsy daga mukaminsa, amma Amurka tana fatan za a farfado da gwamnatin da jama'ar kasa suka zaba da kansu ba tare da bata wani lokaci ba. (Maryam)