Liu Xiaoming ya bayyana cewa, aikin "mamaye cibiyar kasuwanci" da daliban yankin Hongkong suke yi ya saba wa dokokin yankin, tare da kawo illa ga zaman lafiya, da yanayin bunkasuwar tattalin arziki, tare da zubar da mutuncin yankin a idon duniya. Gwamnatin yankin Hongkong da gwamna Leung Chun Ying ke jagoranta ta daidaita aikin "mamaye cibiyar kasuwanci" yadda ya kamata, ta haka a tabbatar da zaman lafiya a yankin tare da kare rayuka da dukiyoyin jama'ar yankin, wannan ya dace da fatan yawancin jama'ar yankin, kana ya shaidawa duniya karfin gwamnatin yankin na gudanar da ayyuka bisa doka.
A nasa bangare, Rimsky Yuen ya bayyana cewa, manufar ziyararsa a wannan karo ita ce yin bayani game da aikin gina cibiyar yanke hukunci da bada hidimar dokoki ta yankin Hongkong ta yadda kasashen duniya za su kara fahimtar halin da ake ciki a yankin. Ya ce, ya kamata gwamnatin Sin da gwamnatin yankin Hongkong su daidaita harkokin yankin, tsoma baki da sauran kasashen duniya suke yi zai kawo illa ga ci gaban demokuradiyya a yankin Hongkong. (Zainab)