in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya gana da gwamnan yankin musamman na Hongkong
2014-11-09 17:28:56 cri
A safiyar yau Lahadi 9 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da gwamnan yankin musamman na Hongkong, Leung Chun-ying, wanda zai halarci kwarya-kwaryar taron shugabannin membobin kungiyar APEC karo na 22 a nan birnin Beijing.

A yayin ganawarsu, shugaba Xi ya saurari rahoton da Leung Chun-ying ya yi dangane da yanayin da ake ciki a yankin Hongkong da aikin da gwamnatin yankin ke gudanarwa, inda Xi ya bayyana cewa, a cikin cikakken zaman taro karo na hudu na kwamitin tsakiyar JKS na 18, an fidda babban buri na gudanar da harkokin gwamnatin kasa bisa doka, inda aka jaddada cewa, za a tabbatar da bin manufar "Kasa daya amma da tsari biyu", da bunkasa yankin Hongkong da Maccau mai dorewa cikin dogon lokaci, da kiyaye moriyar 'yan uwanmu a wadannan yankuna biyu bisa doka. Gudanar da harkoki bisa doka babban tushe ne wajen samun wadata a yankin Hongkong cikin dogon lokaci. Gwamnatin Sin ta amince da kuma nuna goyon baya ga gwamnan yankin musamman da gwamnatin yankin musamman da su aiwatar da ayyukansu bisa doka yadda ya kamata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China