Kamfanin kimiyya da fasaha mai suna Toumaï Hanana Technology na kasar Chadi ya sanar a 'yan kwanakin baya cewa, zai fara sayar da karamar kamfutar hannu samfurin Toumaï kirar kasar ta Chadi.
Wani jami'in kamfanin ya bayyana cewa, an shafe shekaru biyu ana nazarin yadda za a kera kamfuta ta Toumaï, kuma an kashe kudin kasar Chadi Franc miliyan 100(wanda ya yi daidai da kudin Sin Yuan miliyan 1.2), kuma za a sayar da ita a kan Franc dubu 90(kamar Yuan 1200).
Bisa labarin da muka samu daga kamfanonin watsa labaru na kasar Chadi, an ce, za a fara sayar da kamfutar Toumaï ce a N'Djamena, babban birnin kasar, daga bisani nan kuma za a cigaba da sayar da su a duk fadin kasar ta Chadi da ma sauran kasashen Afirka.
A halin yanzu dai, hukumomin ba da ilmi na wasu kasashen Afirka ciki har da Kamaru da Senegal, sun nuna burinsu na sayen kamfutar Toumaï, don haka a yanzu suna shawarwari kan wannan batu.(Danladi)