in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jiragen kasa da Sin ke kerawa na samun karin kasuwa a kasashen waje
2014-09-10 14:29:40 cri
Kamfanin kera jiragen kasa na CSR dake birnin Ziyang na nan kasar Sin ya bayyana cewa, jiragen kamfanin na CSR mai kwarewa a fannin kera jiragen kasa mafiya sauri, na samun karin karbuwa a fadin duniya, yayin da kuma jiragen kasan da Sin ta kera ke kara gaggauta shiga kasashen waje.

Yayin wani bikin baje-koli na kasar Sin da kasashen Asiya da Turai karo na 4, wanda ya gudana tsakanin ranekun 1 zuwa 6 ga watan nan a jihar Xinjiang, an gwada wasu jiragen kasa kirar kamfanin na CSR, jiragen da kuma suka janyo hankalin kamfanoni da dama daga kasashe da yankuna 45 na duniya. Hakan dai ya nuna karfin nazari da kasar Sin ke da shi ta fannin kera jiragen kasa.

Wani jami'in kamfanin na CSR ya bayyana cewa, a halin yanzu ana fitar da jiragen kasa fiye da 600 da kamfanin ya kera zuwa kasashe 23 na nahiyoyin Asiya, da Afirka, da Amurka, da kuma tsibiran Pacific. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China