in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akalla mutane 4 suka mutu yayin da 63 suka jikkata a wani hadarin jirgin kasa a New York
2013-12-02 13:04:45 cri

Akalla mutane hudu ne suka mutu a yayin da 63 suka jikkata a lokacin da wani layin dogo na fasinja ya kaucewa hanyarsa a ranar Lahadi a Bronx a karkarar birnin New York na kasar Amurka, a cewar kafofin watsa labarai na wurin.

Ma'aikatar 'yan kwana kwana ta birnin New York FDNY ta tabbatar da cewa, akalla mutane hudu sun raya rayukansu, kana wasu da dama suna cikin wani mawuyacin hali.

Har wa yau, mutane shida na fama da mummunar kuna, amma da haka rayuwarsu ba ta cikin hadari ba, haka mutane 46 sun ji 'dan rauni.

Jirgin kasan dai ya fita daga hanyarsa a lokacin da yake kusantar tashar layin dogo ta Spuyten-Duyvil dake Bronx a ranar Lahadi da safe da karfe bakwai da rabi bisa agogon wurin, in ji ma'aikatar FDNY tare da bayyana cewa, kusan 'yan kwana kwana dari ne aka tura zuwa inda hadarin ya abku. (Maman Ada) 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China