Wata mace 'yar kunar bakin wake ta tada bam din dake jikinta a tashar jirgin kasa a kudancin kasar Rasha a ranar Lahadin nan 29 ga wata, wanda a nan take ta hallaka mutane 14, in ji mahukuntan kasar.
A kalla mutane 45, ciki har da wata yarinya 'yar shekara 9 suka jikkata sanadiyyar wannan fashewar bam din da ya auku da misalin karfe daya saura kwata na rana, agogon Moscow, a Volgograd, wani gari dake kusa da yankin arewacin Caucasus, in ji jami'an tsaron wannan shiyya.
'Yar kunar bakin waken dai ta tada bam din dake jikinta a gaban kofar shiga inda na'urori ke tantance ko akwai makami a jikin fasinjoji na tashar jirgin kasan, in ji kafar yada labaran kasar.
Gwamnan garin Volgograd, Sergei Bozhenov ya ce, kwanaki uku na sabuwar shekara da za'a shiga, za'a kebe su zama ranaikun makokin na wadanda wannan mummunar hari ya rutsa da su.
Shugaba Vladimin Putin kuma ta bakin kakakinsa Dmitry Peskov ya ba da umurnin cewa, gwamnati ta dauki dukkan matakan tsaron da suka dace wajen taimaka wa wadanda suka jikkata sanadiyyar harin. Sannan ya kuma umurci kwamitin bincike da ya gudanar da ayyukansa yadda ya kamata, da haka za a tabbatar da tsaro a kasar.
Wannan harin dai shi ne na biyu da ya girgiza garin Volgograd kwanan nan. Watanni biyu da suka gabata wato a watan Oktoban da ya gabata, wata mace 'yar kunar bakin wake ta tada bam din dake jikinta a wani bas, inda anan take ta hallaka mutane 7, wassu da dama kuma suka jikkata.
Ita wadda ta kai harin na watan Oktoba, daga baya an tantance ta a matsayin uwargidan Dmitry Sokolov, wani mutum daga karkarar Moscow wanda daga baya ya shiga kungiyar 'yan tawaye a jamhuriyar Dagestan dake kudancin Rasha. (Fatimah)