in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin jihar Kano dake arewacin Najeriya zata gina hanyar karkashin kasa cikin wannan shekara ta 2014
2014-01-02 10:55:31 cri
A kokarin da take yi na tabbatar da ganin birnin Kano ya shiga jerin manyan biranen duniya, gwamnatin jihar Kano zata bayar da kwangilar gina titin karkashin kasa a wannan sabuwar shekara ta 2014.

Gwmanan jihar Kanon Injiniya Rabi`u Musa kwankwaso shi ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake karbar bakuncin ministan kasa da raya birane na tarayyar Najeriya Architect Musa Mohammad Sada.

Injiniya Rabi` u Musa kwankwaso ya ce tuni gwamnati ta kammala tsare-tsarenta game da wannan katafaren titin irin sa na farko a tarayyar Najeriya.

Yace aikin zai taso ne daga titin Malam Aminu Kano zuwa unguwar Gadon kaya dake cikin birnin Kano, inda ya ce idan an kammala aikin zai taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa a wannan yanki.

Injinya Rabi`u Musa Kwankwaso ya ci gaba da cewa gwamnati na nan na nazarin kamfanin da za a baiwa aikin, bayan an tantace nagartarsa.

Ya kara da cewa gina wannan titi yana daya daga cikin manufofin gwamnatinsa na kawata birane da karkara, ya ce a yanzu haka gwamnati ta yi nisa wajen gina sabbin birane guda uku a bangarori daban daban na shigowa cikin birnin Kano.

Gwamnan ya tabbatar da cewa kafin karewar wa`adin mulkinsa a 2015 zai kammala dukkan ayyukan daya faro.

Ya ci gaba da cewa zayyanawa ministan irin ayyukan da yake gudanarwa yanzu haka a sassan jihar daban daban. Wadanda suka hadar da gadojin sama a cikin birnin Kano da wani kamfanin kasar Sin ke gudanarwa, da kuma ayyukan raba tituna a birni da yankunan kananan hukumomin jihar 44 wanda ya zuwa yanzu ayyukan sun lankwame tsabar kudi sama da naira buliyan hamsin.

Da yake nasa jawabin ministan kasa da raya birane na tarayyar Najeriya Architect Musa Sada ya ce ya zo jihar Kano ne domin tattaunawa da gwamnan akan hanyoyin da yake bi wajen warware matsalolin muhalli ga al`ummar jihar.

Ministan ya bayyana gamsuwa bisa irin nasarorin da gwamnatin jihar Kano ta samu ta fuskar bunkasar birane da yankunan karkara.

Ya tabbatar da cewa majalissar lura da harkokin ci gaban birane ta kasa zata hada kai da gwmanatin Kano wajen warware matsalolin muhalli a birane da yankunan karkara na tarayyar Najeriya.

Bincike dai ya tabbatar da cewa sama da magidanta 300 ne a cikin birnin Kano kadai suka rasa muhallinsu sakamakon aikin fadada tituna da kuma haramta gine-gine a filayen da aka samar ba tare da masaniyar gwamnati ba.(Garba Abdullahi Bagwai)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China