An dai kai ruwa-rana tsakanin kungiyoyin biyu kafin kammalar wasan. Ko da yake alkalin wasan ya hana kwallaye biyu da kulaflikan suka ci a farko farkon wasan.
A minti na 21 da take wasan ne kuma, dan wasan Mainz Shinji Okazaki ya sawa abokin wasan sa Elkin Soto wata kwallo, wadda nan take Soto ya zura ta a ragar Munich.
Mintuna biyu da hakan ne kuma Bayern Munich din ta farke wannan kwallo ta hannun dan wasan ta Bastian Schweinsteiger, wanda ya saka kwallo a zaren Mainz ta hanyar bugun free kick.
Haka dai aka yi ta gumurzu har ya zuwa daf da karshen wasan. Ana kuma daf da tashi ne Arjen Robben ya samu nasarar jefa kwallo ta 2 ga Bayern Munich, aka kuma tashi Bayern na da kwallo 2 Mainz na da 1.
Da kuma wannan sakamako, Bayern din ta kara yawan tazarar maki tsakanin ta da Wolfsburg dake matsayi na biyu da maki 11, bayan wasannin da aka buga a ranar Asabar. Ya yin da Mainz ta sake dibar rashin nasara a karo na 5 a jere, ta kuma sauka zuwa matsayi na 12 a teburin gasar ta Bundesliga bayan wasannin ranar Asabar.
Yanzu haka dai baya ga Bayern da Wolfsburg dake matsayi na 1 da na 2, akwai kuma Bayer Leverkusen, da Borussia Mönchengladbach, da FC Schalke, dake matsayi na 3 da na 4 da na 5.
Can a kasan teburin kuwa Borussia Dortmund ce a matsayi na 17 sai kuma SC Freiburg dake a matsayi na 18.