Bisa wannan kididdiga, kasar ta Zambia ta daga, daga matsayi na 15 a Afirka, kuma ta 62 a duniya, ya zuwa matsayi na 10 a Afirka ta kuma 46 a duniya.
Kasar ta Zambiya wadda ta lashe kofin nahiyar Afirka na shekarar 2012, ta samu wannan ci gaba ne, sakamakon kwazon da ta nuna a wasannin share fagen gasar nahiyar mai zuwa. Za kuma ta buga wasannin ta ne a rukunin B, tare da kasashen Tunisia, da Cape Verde da janhuriyar Dimokaradiyyar Congo, a gasar da za a fara cikin watan Janairun dake tafe a kasar Equatorial Guinea.