in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai tsaron bayan kulaf din kasar Faransa zai yi ritaya
2014-12-24 10:29:55 cri
Tsohon dan wasan kasar Faransa Eric Abidal, ya bayyana niyar sa ta yin ritaya daga taka leda, bayan wasan da zai bugawa kulaf din sa na Olympiacos a ranar Juma'a.

Dan wasan, wanda ke tsaron baya ga Olympiacos na kasar Girka ya bayyana cewa, wannan mataki muhimmi ne matuka a rayuwar sa, kasancewar a wannan gaba ne zai rataye takalman sa na kwallo, bayan taka leda a kulaflika da dama ciki hadda Barcelona na Sifaniya.

Abidal, wanda ya fara taka leda a Olympiacos watanni 6 da suka gabata, ya bayyanawa wani taron manema labaru cewa, ya samu gayyata daga Barcelona da Olympiacos game da ci gaba da wasa, amma bai bayyana matsayar sa game da hakan ba.

Tuni dai dan wasan ya bugawa wasanni 8, cikin 14 a gasar Super League, ya kuma taka leda a dukkanin wasannin gasar zakarun turai 6 da Olympiacos din ya buga.

Abidal, wanda ya fara buga gasannin ajin kwararru a shekarar 2000 a kulaf din Monaco, ya taba lashe gasar ajin farko har sau 3, lokacin da yake kulaf din Lyon. Ya kuma bugawa kasar Faransa wasa har karo 67, ciki hadda wasannin da aka buga a gasar cin kofin duniya na Faransa a shekarar 2006.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China