in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon kocin kungiyar Chelsea ya zama sabon kocin Ghana
2014-12-05 10:01:26 cri
A ranar 28 ga watan Nuwanbar da ya gabata ne hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta kasar Ghana, ta sanar da cewa tsohon kocin kungiyar Chelsea dake kasar Ingila Avraham Grant, ya zama sabon kocin kungiyar kwallon kafar kasar Ghana, tuni kuma ya daddale yarjejeniyar shekaru biyu da hukumar kwallon kafar ta Ghana.

Tsohon kocin kungiyar kwallon kafar Ghana ya yi murabus ne a watan Satumba, kafin daga bisani hukumar kwallon kafar kasar ta zabi Grant a matsayin sabon kocin bayan watanni biyu.

Game da hakan shugaban hukumar kwallon kafar Ghana ya bayyana cewa, burin Grant shi ne ya jagori kungiyar kasar Ghana wajen cimma kyakkyawan sakamako a gasar cin kofin Afirka da za a gudanar a badi.

Wannan ne dai karo na biyu da Grant ya karbi aikin horas da kungiyar wata kasar waje. Inda a baya ya taba zama kocin kasar Isra'ila tsakanin shekarar 2002 zuwa 2006. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China