in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Equatorial Guinea ce za ta dauki bakuncin gasar cin kofin Afirka
2014-11-21 14:42:28 cri

Wata sanarwa da hukumar kula da kwallon kafar nahiyar Afirka CAF ta fitar, ta bayyana kasar Equatorial Guinea a matsayin kasar da za ta maye gurbin Morocco, a karbar bakuncin gasar kwallon kafar Afirka dake tafe a farkon shekarar 2015 dake tafe.

Sanarwar wadda ta fito daga ofishin kwamitin zartaswar hukumar ta CAF a ranar Jumaar da ta gabata, ta tabbatar da gudanar gasar kamar yadda aka tsara, wato daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watana Fabarairun shekarar ta 2015.

Yanzu hakan dai kasar Equatorial Guinea na da tikitin buga wannan gasa, kuma batun bata damar karbar bakuncin wannan gasa ya biyo bayan janyewar da kasar Morocco ta yi ne daga karbar bakuncin ta.

Kafin hakan dai Moroccon ta bukaci a dade gudanar da gasar sakamakon tsoron ta ga yaduwar cutar Ebola. Matakin da bai yiwa hukumar ta CAF dadi ba.

A baya ma dai kasar Equatorial Guinea ta karbi bakuncin gasar kwallon kafar nahiyar Afirka a shekarar 2012 da hadin gwiwar kasar Gabon, a yanzu kuma an tsara buga gasar a biranen Malabo, da Bata, da Mongomo da kuma birnin Ebebiyin.

Kaza lika bisa tsarin gasar, za a fidda kurunonin kasashen da zasu fafata a ranar Laraba 3 ga watan Disambar dake tafe a birnin Malabo.

Kungiyar AU ta jinjinawa Equatorial Guinea bisa amincewa ta karbi bakuncin gasar AFCON

Shugabar hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma, ta jinjinawa kasar Equatorial Guinea bisa amincewar da ta yi, na ta karbi bakuncin gasar cin kofin Afirka dake tafe a badi. Zuma ta kuma yi kira ga daukacin mambobin AU, da su baiwa gasar cikakken goyon baya.

Da take karin haske game da matsayin da Equatorial Guinea ta dauka na daukar dawainiyar gasar, Zuma ta ce hakan ya nuna hadin kai dake tsakanin kasashen nahiyar Afirka.

Kaza lika uwargida Zuma ta ce sam bai kamata cutar Ebola ta hana gudanar gasar kwallon kafar nahiyar ba. Ta ce Afirka na fuskantar tarin kalubale, ciki hadda batun ta'addaci, da yaki da yaduwar cutar HIV/ Sida, da sauran matsaloli wadanda da hadin kan dukkanin al'ummunta, ake fatan magance su baki daya.

Zuma ta kara da cewa AU da hukumar CAF na da matsaya guda game da bunkasa kawancen nahiyar Afirka. Sanarwar ta ce ya yin tattaunawar da CAF din ta gudanar a watan Satumbar da ya shude a birnin Addis Ababan kasar Habasha, mahukuntan hukumar sun bayyana matukar goyon bayan su ga yunkurin da ake yi na yaki da cutar Ebola. Don haka a cewar sanarwar, sam bai dace cutar Ebola ta kasance tarnaki ga gudanar wannan muhimmiyar gasa mai hada kai, da hada zumunta tsakanin kasashen nahiyar Afirka.

Daga nan sai sanarwar ta bayyana kudurin kungiyar ta AU na baiwa hukumar CAF dukkanin hadin kai da goyon baya, tana mai jaddada kira ga daukacin kasashe mambobin ta da su marawa Equatorial Guinea baya, domin cimma nasarar gasar.

Kafin hakan dai shugaban hukumar ta CAF Issa Hayatou ya bayyana amincewar mahukuntan kasar Equatorial Guinea, na karbar bakuncin gasar dake tafe, jim kadan bayan kammalar tattaunawar sa da shugaba Teodoro Obiang Nguema, na Equatorial Guinea a ranar Juma'ar da ta shude. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China