Rahotanni sun ce 'yan kallon sun rika jefa ababen wasan wuta cikin filin wasan, lamarin da ya tilasa tsayarda buga kwallo har na kusan mintuna 10, kafin daga bisani jami'an tsaro sun fidda wani sashe na 'yan kallon wajen filin, a kuma ci gaba da taka leda.
Daga karshe dai an tashi wasan kunne doki 1 da 1. Ana kuma hasashen cewa mai yiwuwa kwamitin ladaftarwa na hukumar kwallon kafar turai, ta hukunta hukumar kwallon kafar Croatia, kasancewar ba wannan ne karon farko da 'yan kallon kasar suka taba tada hargitsi a filin wasa ba.
Akwai kuma hasashen kulaf din kasar ta Croatia ya buga wasan sa na gaba a gida da Norway, na ranar 28 ga watan Maris mai zuwa ba tare da 'yan kallo ba. Ya zuwa yanzu dai Croatian ce ke saman teburin rukunin H, a wasannin na share fagen gasar kwallon kafar kasashen nahiyar turai.(Saminu Alhassan)