Rahotanni sun bayyana cewa za a rika baiwa jagororin addinan tallafin kudi a kowane wata tun daga watan Janairun dake tafe, ko da yake sun ce wadanda aka samu da karya dokokin da suka shafi addini za su rasa damarsu ta karbar tallafin, kana mahukuntan yankin ba su bayyana dalilin fito da wannan tsari ba.
Ana dai sa ran gudanar da wannan tsari na gwaji a tsahon shekara guda.
Yankin Ningxia dai na kunshe ne da al'ummar karamar kabilar Hui, kuma kaso daya bisa uku na daukacin al'ummar yankinsu miliyan 6 da rabi musulmi ne, akwai kuma masallatai sama da 3,700 a yankin, baya ga sauran majami'u da kuma wuraren bauta na addinin Budda. (Saminu Hassan)