in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yankin Macau ya cimma nasarori da dama, in ji Shugaba Xi
2014-12-19 20:32:01 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, yankin musamman na Macau ya cimma nasarori da dama a fannonin jin dadin jama'a da tattalin arziki tun lokacin da yankin ya dawo karkashin ikon kasar Sin shekaru 15 da suka gabata.

Shugaba Xi ya bayyana hakan ne yau Jumma'a a yankin Macau, yayin cikar yankin shekaru 15 da dawowarsa hannun ikon kasar Sin. Yana mai cewa, yankin ya cimma wadannan nasarori ne karkashin tsarin nan na kasa daya bisa tsarin mulki iri biyu da kuma dokoki na tushe da ake amfani da su yadda ya kamata.

Bugu da kari, shugaba Xi ya ce, ana danganta nasarorin da yankin Macau ya samu ga hadin kai da aikin tukuru na gwamnatin yankin, kishin al'ummar yankin da cikakken goyon bayan da yake samu daga gwamnatin tsakiya da kuma daukacin kungiyoyin kabilu dake kasar Sin.

Ya ce, yankin Macau yanzu ya kasance yankin dake tafiyar da harkokin kansa cikin hadin kai da himma da kwazo wanda ya tsaya tsayin daka wajen gina yankin da kuma manufofin kasa daya bisa tsarin mulki iri biyu.

A gobe Asabar ne ake saran shugaba Xi zai halarci bikin kaddamar da gwamnatin yankin karo na hudu, bikin da zai gudana a yankin musamman din na Macau na kasar Sin. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China