in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da jami'an yankin musamman na Hongkong da Macau
2013-03-18 16:15:03 cri

Safiyar yau ranar 18 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da gwamnan yankin musamman na Hongkong mai cin gashin kansa Leung Chun Ying da na yankin musamman na Macau Fernando Chui SaiOn, wadanda suka halarci bikin rufe taro karo na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 12.

Xi ya jaddada dangantakar dake tsakanin babban yanki da Hongkong da Macau. Kuma ya ce, samun bunkasuwar al'ummar Sinawa na bukatar hadin gwiwa tsakanin bangarorin uku.

Xi Jinping ya ce, Leung Chun Ying ya gabatar da manufarsa ta samun bunkasuwa mai dorewa tare da yin kyautatuwa, wadda ta samu goyon bayan jama'ar yankin Hongkong. Ya zuwa yanzu, abin da aka sa gaba shi ne aiwatar da wannan manufa yadda ya kamata karkashin jagorancin gwamnan yankin da karamar gwamnatin yankin Hongkong da haka kuma tare da hadin gwiwar jama'ar yankin Hongkong.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, yankin Macau na cikin hali mafi kyau a tarihi. Amma zai fuskanci kalubaloli nan gaba. Yana fatan karamar gwamnatin yankin Macau da bangarori daban-daban da su kara karfin tinkarar kalubaloli masu zuwa da kuma yin amfani da zarafi mai kyau domin fitar da wani matakin warware matsalolin dake kawo cikas ga samun bunkasuwa, ta yadda za'a kafa tubali mai kyau ga yankin Macau domin samun bunkasuwa mai dorewa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China