in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan jarin da Sin ta saka kai tsaye a kasashen waje ya kai dalar Amurka biliyan 87.8
2013-09-10 16:22:50 cri
A ranar 9 ga wata, bisa alkaluman da ma'aikatar kula da harkokin kasuwanci, da hukumar kididdiga, da hukumar kula da kudaden ajiya na kasashen waje ta kasar Sin suka bayar a jimlace, an ce, yawan jarin da Sin da ta saka kai tsaye a kasashen waje a bara ya karu, inda a yanzu ya kai dalar Amurka biliyan 87.8, wato ke nan, kasar Sin ta zama daya daga cikin manyan kasashe 3 da suka fi ragowar kasashe saka jari a kasashen duniya.

Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, jarin da aka saka kai tsaye a duniya, ya ragu da kashi 17 cikin 100 a bara idan aka kwatanta da na shekarar 2011, yawan jarin da kasar Sin ta saka kai tsaye zuwa kasashen waje ya zama abin tarihi, bisa karuwar da ya yi da kashi 17.6 cikin 100, wato ke nan kasar Sin ta dau matsayi na uku bayan kasashen Amurka da Japan wadanda suke sahon gaba wajen saka jari a kasashen waje.

Ya zuwa karshen shekarar bara, jarin da Sin ta saka kai tsaye ya shafi fannoni da dama, na raya tattalin arzikin al'umma, cikinsu, har da sana'ar hada-hadar kudi, da hakar ma'adinai, da sauran fannoni, kuma yawan jarin da ta saka ya zarce dalar Amurka biliyan 10.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China