in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron kasar Sin ya yi shawarwari da takwaransa na Zimbabwe
2014-10-10 10:26:50 cri
Jiya Alhamis 9 ga wata, a nan birnin Beijing, memban majalisar gudanarwa ta Sin, kana ministan tsaron kasar Sin Chang Wanquan ya yi shawarwari da takwaransa na Zimbabwe Sydney Sekeramayi.

A lokacin shawarwarin, Mr. Chang ya ce, akwai dankon zumunci tsakanin Sin da Zimbabwe, rundunonin sojan kasashen biyu sun yi mu'amala da juna sosai, kuma an tura tawagogi na bangarorin biyu zuwa kasashen juna sau da dama, tare da samun babban sakamako wajen hadin gwiwa a fannonin horar da ma'aikata da sauransu. Don haka rundunar sojan Sin na fatan ci gaba da karfafa mu'amala tsakanin ta da Zimbabwe, domin kara ba da gudummawa ga bunkasa kyakkyawar dangantaka tsakanin su.

A nasa bangare, minista Sekeramayi ya nuna godiyarsa ga gwamnatin Sin wajen taimakawa kasar a fannonin siyasa, kayayyaki da sauransu. Da fatan rundunonin sojan kasashen biyu za su karfafa hadin gwiwa da zurfafa dangantaka tsakaninsu yadda ya kamata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China