in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 6388 ne suka mutu a sakamakon cutar Ebola
2014-12-11 10:59:51 cri
Bisa labarin da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta bayar, an ce, ya zuwa ranar 7 ga watan Disamba, ana zaton mutane 17942 ne suka kamu da cutar Ebola a yankin yammacin Afirka, yayin da mutane 6388 daga cikinsu suka mutu.

A halin yanzu, kasashen Guinea, Liberia da Saliyo da ke fama da cutar ta Ebola suna ci gaba da yin kokari killace dukkan mutanen da suka kamu da cutar, da binne gawawwakin mutanen da suka mutu a sakamakon cutar yadda ya kamata kafin ranar 1 ga watan Janairu na shekara mai zuwa. Tuni dai shugabar kasar Liberia Ellen Johnson-Sirleaf ta yi kira da a gudanar da aikin "kawar da cutar Ebola", inda ta bukaci jama'ar kasar da su dauki matakan hana kamuwa da cutar ta Ebola.

A ranar 9 ga wata, manzon musamman na babban sakataren MDD mai kula da batun cutar Ebola David Nabarro ya yi nuni da cewa, akwai sauran tafiya ga kasashen duniya kafin a kawar da cutar Ebola, don haka bai kamata a sassauta kokarin da ake yi ba. A halin yanzu, ayyukan tinkarar cutar ta Ebola sun fara yin tasiri, kuma nasarar kawar da cutar ya dogara ne kan yadda jama'a suka canja ayyukansu na yau da kullum don rage hadarin kamuwa da cutar.

Daga ranar 10 zuwa 11 ga wata ne hukumar WHO, bankin duniya, bankin raya Afirka da kungiyar kiwon lafiya ta yammacin Afirka suka gudanar da taron koli a birnin Geneva inda suka tattauna da kafa tsarin kiwon lafiya mai inganci a kasashe masu fama da cutar Ebola na yammacin Afirka. Babbar direktan hukumar WHO Margaret Chan ta bada shawara a gun taron cewa, kamata ya yi kasashe uku na yammacin Afirka da ke fama da cutar su ba da muhimmanci a bangaren bincike da tinkarar sabbin cututtuka masu yaduwa a tsarinsu na kiwon lafiya, da tabbatar da cewa, iyalai sun samu hidimar kiwon lafiya, kana unguwoyi su kara taka muhimmiyar rawa wajen tinkarar cutar, da kara samar da kayayakin kiwon lafiya masu inganci da samar da hidimar kiwon lafiya da ta dace, da tabbatar da samar da ruwa mai tsafa, da hasken wutar lantarki da magunguna da sauransu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China