Yayin isar su kasar, jami'an wadanda suka kunshi likitoci da masu aikin jiyya, sun samu tarba daga jakadar Najeriya a Laberiyan Chigozie Obi-Nnadozie.
Da yake karin haske game da ayyukan da tawagar za ta aiwatar, shugaban shirin tallafawa yaki da cutar ta Ebola a yammacin Afirka Dr. Julius Oketta, ya ce jami'an za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar. Matakin da ake fatan zai bada damar kakkabe birbishin ta daga sassan kasar.
Ana kuma sa ran tawagar za ta kafa cibiyoyin jiyyar cutar a yankunan karkara, musamman wuraren da ake ci gaba da samun masu kamuwa da cutar ta Ebola.(Saminu)