Wani wakili na musamman na magatakardan MDD David Naborro ya yi kira a kan kasashen duniya da su kara ba da guddumuwar gadaje da kwararrru da cibiyoyin kula da marasa lafiya, musamman a yammacin Saliyo da arewacin Guinea domin murkushe cutar Ebola.
Nabarro ya shaidawa wani taron manema labarai cewar, ana bukatar karin ma'aikata daga kasashen waje domin tallafawa gwamnatocin kasashen a yakin da suke yi da cutar ta Ebola.
Ya ce, yawan adadin sabbin wadanda suka harbu da cutar na raguwa sosai, musamman a wasu sassa na Liberia a wajen Monrovia da kuma gabashin Saliyo wadanda a watannin Satumba da Agusta suka zanto wurare da cutar Ebola ta yi kamarin gaske.
Nabarro ya kara da cewar, a yanzu cutar ta fi kazamta a yammacin Saliyo da arewacin Giunea. (Suwaiba)