Kasar Namibiya ta fara daukar ma'aikatan kiwon lafiya domin taimakawa kasashen yammacin Afrika dake fama da cutar Ebola.
Sakataren din din din na ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Namibiya, mista Andrew Ndishishi ya sanar a ranar Litinin cewa, ma'aikatar kiwon lafiya na daukar malaman asibiti, kwararru kan cututtuka masu yaduwa, ma'aikatan ba da jinya, kwararrun dakunan bincike da sauran ma'aikatan lafiya a matakai daban daban domin amsa kiraye kirayen kungiyar tarayyar Afrika (AU) wanda ta bukaci kasashe mambobinta da su taimaka da jami'an kiwon lafiya domin yaki da annobar cutar Ebola. (Maman Ada)