Bisa labarin da aka bayar, an ce, a cikin wadannan mutane uku, daya ya zo cibiyar ce da kansa bayan ya fara jin wasu alamu a cikin 'yan kwanakin da suka wuce, dayan kuma cibiyar kula da harkokin cutar Ebola ta kasar Liberia ce ta kai shi cibiyar ta Sin, yayin da daya kuma wani asibitin dake kasar ya kai shi zuwa cibiyar.
Shugaban sashen kula da harkokin sa ido kan mutanen da ake zaton sun kamu da cutar ta Ebola na cibiyar Ren Xiaobao ya bayyana cewa, a cikin wadannan mutanen uku, wani matashi ya tabbatar da cewa, ya taba wani mutum da ya mutu a kwanaki uku da suka gabata a sakamakon cutar Ebola. Inda wannan matashi ya fara jin zazzabi da ciwon kai da sauran alamomin kamuwa da cutar.
A halin yanzu, cibiyar bada jinya ga wadanda suka kamu da cutar Ebola ta kasar Sin ta tsara shirin sa ido kan mutanen uku bisa ga alamun da suka nuna, tare da ba su jinya. Ya zuwa yanzu cibiyar ta dauki jinin mutanen uku, zuwa cibiyar yin bincike ta wurin don tabbatar da cewa ko sun kamu da cutar ta Ebola ko a'a. (Zainab)