Wang Yi ya ce, kasar Sin da kungiyar ASEAN suna da karfin tabbatar da zaman lafiya da na karko a yankin. Ya ce, an cimma daidaito a gun taron ministocin harkokin waje a wannan karo, na ci gaba da aiwatar da sanarwar ayyukan da bangarori daban daban suka yi a yankin tekun kudancin kasar Sin, da kuma yin kokarin cimma ka'idojin ayyuka a yankin cikin hazari.
Ban da wannan kuma, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin da kungiyar ASEAN sun tattauna batun yankin cikin lumana, abin da ya sa sauran kasashen waje ke iya sa ido a kan batu, amma a ba'a amincewa da su tsoma baki a ciki ba. (Zainab)