Wani masanin kimiyya na jami'ar Oxford Adrian Hill, ya ce, akwai alamun nasara game da nau'o'in alluran rigakafin cutar Ebola 2 da aka yi gwajin su.
Mr. Hill wanda ya bayyana hakan yayin wani taron masana kan rigakafin cututtukan Afirka da ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya, ya kara da cewa, an yi gwajin alluran ne kan wasu mutane 80 a kasar Mali. Bisa jimilla kuma an yi wa mutane 200 gwajin wadannan allurai a duniya baki daya.
A cewarsa, ana sa ran fara fitar da alluran rigakafin zuwa kasashen yammacin Afirka nan da watan Janairu mai zuwa.
Hill ya ce, manyan cibiyoyin sarrafa magunguna dake Birtaniya da gwamnatin Amurka, da sauran sassa da kungiyoyi masu zaman kansu ne suka yi hadin gwiwar samar da wannan allura ta rigakafi, matakin da ya ce zai yi matukar taimakawa, wajen karfafa yakin da ake yi da yaduwar cutar.
Tuni dai hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce, cutar Ebola ta hallaka mutane 6,928 a kasashen Liberia, da Guinea da kuma Saliyo. Yayin da kuma wasu mutane 16,000 ke dauke da wannan cuta, wadanda kuma ke fuskantar barazanar rasa rayukansu muddin ba a dauki wani mataki na tallafa musu ba. (Saminu)