Bisa kididdigar ta WHO daga watan Fabarairun da ya shude ya zuwa yanzu, a kalla mutane 16203 ne suka kamu da cutar, yayin da ta hallaka mutane 6943.
Don gane da karuwar adadin wadanda cutar ta hallaka cikin 'yan kwanakin nan, kakakin hukumar ta WHO ya bayyana cewa, hakan na da nasaba da sabon adadin da kasar Liberia ta samar, wanda hakan ya ba da sabbin sakamako ga alkaluman rasuwar mutanen cikin 'yan kawanaki kadan.
Bugu da kari, hukumar WHO ta bayyana cewa, wahalar gudanar da aikin kididdigar wadanda cutar ta kashe a baya shi ma wani babban kalubale ne, an kuma yi imanin cewa, adadin rasuwar mutanen na hakika ya haura adadin da aka fitar a baya. (Maryam)