Magatakardan MDD Ban Ki-moon ya nada Abdou Dieng na kasar Senegal a matsayin mai kula da hanyoyin da za'a bi a dakile cutar Ebola a kasar Guinea a karkashin tsarin MDD na daukar matakai na gaggawa domin tunkarar cutar Ebola.
A halin da ake ciki, Dieng zai maye gurbin Marcel Rudasingwa. Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq, wanda ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi ga manema labarai ya ce, Mr. Dieng zai ci gaba da tafiyar da ayyukan MDD a kasar ta Guinea tare da taimakon gwamnatin kasar da sauran kasashe domin kara kaimin yakin da ake yi da cutar Ebola. (Suwaiba)