An buga bayani game da wannan nasarar da kamfanin na NIH ya samu ne dai a wata mujallar kiwon lafiya ta kasar Amurka. An kuma ce sashen manazarta kan cututtuka masu yaduwa na kamfanin, da masu bincike na kamfanin GSK ne suka samar da allurar ta hanyar ajiye wasu sinadarai daga kwayoyin cutar ta Ebola cikin jikin bil'adama, kafin daga karshe sarrafa su, su kuma fidda wannan allura ta riga kafi.
Yanzu haka dai ana fatan a nan gaba, manazarta za su kara yin gwaji kan nagartar wannan allura ta riga kafin cutar Ebolan a kasar Amurka, da kuma wasu kasashe yammacin Afirka. (Zainab)