in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a ci gaba da baiwa yaki da Ebola cikakkiyar kulawa, in ji shugaban ECOWAS
2014-11-27 10:33:23 cri

Shugaban kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka Kadre Desire Ouedraogo, ya ce, ECOWAS ta fidda wasu manufofi 3 na ci gaba da yakin da ake yi da cutar Ebola a yammacin Afirka.

Ouedraogo wanda ya bayyana hakan yayin wani taron karawa juna sani, da aka shiryawa wasu jami'an sa kai su 150, wadanda za su shiga wannan aiki a kasashen Guinea, da Liberia da Saliyo, ya kara da cewa, matakan sun hada da na kandagarki, da dakile yaduwar cutar, tare kuma da kawo karshen cutar baki daya.

Ya ce, sabbin matakan, kari ne kan sauran manufofin da ake aiwatarwa domin dakile yaduwar wannan cuta, da tuni ta hallaka mutane 5,444 a kasashe 3 na yankin.

Daga nan sai ya jaddada aniyar kungiyar ta ECOWAS da hadin gwiwar kasashe mambobin ta, na ganin an aiwatar da manufofin da za su taimaka, a kai ga kawo karshen yaduwar wannan cuta baki daya.

Bullar wannan cuta ta Ebola dai ya haifar da tarin kalubale ga kasashen duniya baki daya, duba da yadda ta tsallaka har wasu kasashen Turai kamar Amurka da Sifaniya da Norway, bayan mummunan ta'adin da ta yi a wasu kasashen yammacin nahiyar ta Afrika. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China