in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar WHO ta tattauna da shugabannin Mali game da tunkarar Ebola
2014-11-25 13:13:03 cri

Darektan hukumar lafiya ta duniya WHO Margaret Chan ta ziyarci kasar Mali a karshen makon da ya gaba domin tattaunawa da hukumomin kasar a kan hanyoyin da suka dace a yi amfani da su domin dakile cutar Ebola, wacce a kalla ta rigaya ta hallaka mutane 5 a kasar ta Mali dake Afrika ta yamma.

Kakakin MDD Stephane Dujarric ya ce, ziyarar ta madam Chan ta biyo bayan gwamnatin kasar ta bayar da tabbacin cewar, ta gano wani 'dan kasar ya kamu da Ebola, kana kuma ana gudanar da gwaji a kan wadansu majiyyata guda biyu, kalaman gwamnatin ya haifar da fargabar ci gaba da yaduwar cutar ta Ebola mai saurin kisan bi'adama.

Kakakin MDD Stephane Dujarric ya kara da cewar, shugabar hukumar lafiyar duniya ta ziyarci wata cibiyar kula da lafiyar masu dauke da cutar Ebola a Bamako, kuma ta gana da shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita da kuma firaministan kasar Moussa Mara da sauran kusoshin kasar, a inda suka tattauna a kan kokarin da kasar ta Mali ke yi na dakusar da yaduwar cutar, da kuma hanyoyin da hukumomin MDD za su dauka domin kara kaimin tallafinsu ga kasar ta Mali.

A yanzu an yanke shawarar cewar, hukumar MDD mai daukar matakin gaggawa a kan cutar Ebola UNMEER za ta bude ofishinta a kasar ta Mali.

Babban darektan shirin ciwon Sida Michel Sidibe, wanda ya ziyarci kasar tare da shugabar hukumar lafiya ta duniya ya bayyana cewar, kwanaki 15 a nan gaba na cike da mahimmanci a wajen dakile cutar Ebola a Mali. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China