in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane biyu sun kamu da cutar Ebola a Mali
2014-11-26 10:20:02 cri

Wasu karin mutane 2 sun harbu da cutar Ebola a kasar Mali, lamarin da ya sanya adadin wadanda ke dauke da cutar a kasar karuwa zuwa mutane 8.

Hakan kuwa na zuwa ne gabanin shirin bude ofishin yaki da Ebola na MDD a kasar, kamar dai yadda kakakin MDDr Stephane Dujarric ya shaidawa manema labaru a jiya Talata.

Da yake karin haske game da matakan da ake dauka na dakile yaduwar cutar, Dujarric ya ce, matakan gano wadanda suka yi mu'amala da masu dauke da cutar sun yi matukar tasiri, kuma bisa makamantan su da aka aiwatar a Senegal da Najeriya, sakamakon ya nuna matukar nasarar da za a iya samu wajen dakile yaduwar cutar a Mali.

A daya hannun kuma, gwamnatin kasar ta Mali da hadin gwiwar hukumar lafiya ta WHO za su gudanar da wani zama na tattauna da masu ruwa da tsaki daga kasar Guinea, da nufin daukar matakan dakile yaduwar cutar tsakanin kasashen biyu.

Ana dai sa ran bude ofishin MDD na yaki da cutar ta Ebola ne a yau Laraba, a birnin Bamakon kasar ta Mali, a ci gaba da daukar matakan agazawa kasar wajen kawo karshen yaduwar Ebola baki daya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China