in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha za ta tura ma'aikatan sa kai 210 zuwa kasashen dake fama da Ebola
2014-11-26 13:32:47 cri

Kasar Habasha ta sanar a ranar Talata cewa, za ta tura kimanin ma'aikatan sa kai 210, nan da makwanni biyu zuwa kasashen yammacin Afrika dake fama da cutar Ebola.

Ma'aikatan sa kan 210, an zabe su daga cikin ma'aikatan sa kai dubu daya da dari da aka yi rijista, in ji Ahmed Imano, shugaban harkokin sadarwa a ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Habasha a yayin da yake hira da manema labarai a birnin Addis Abeba. Wadannan mutane sun hada da ma'aikatan lafiya, shugabannin hukumomin kiwon lafiyar jama'a, masanan cututtuka masu yaduwa, kwararrun dakunan bincike, masu ba da horo a fannin kiwon lafiya da sauransu. Za'a tura su har zuwa tsawon watanni uku a cikin kasashe uku da cutar ta fi tsanani wadanda suka hada da Liberiya, Saliyo da Guinea.

A cewar Ahmed Imano, kasar Habasha ta amsa kiraye kirayen kungiyar tarayyar Afrika (AU) da kuma kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO), kuma ta dauki niyyar wajen taimakawa kasashen yammacin Afrika dake fama da cutar Ebola ta hanyar tura ma'aikatan lafiya da taimakon kudi na dalar Amurka dubu dari biyar.

Haka kuma mista Amino ya tunatar da matakan da kasarsa ta dauka bisa tsarin yin rigakafin cutar Ebola, har ma da matakin yin bincike kai tsaye a filin jiragen saman Addis Abeba, da ma wasu ayyukan fadakarwa da na ba da horo daga dukkan fannoni. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China