in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na da shirin kafa cibiyar leken asiri don yaki da ta'addanci
2014-10-27 16:24:28 cri

Za a tattauna kan daftarin dokar yaki da ta'addanci ta kasar Sin a yayin taro karo na 11, na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da za a kira yau Litinin 27 ga wata, daftarin dake kunshe da kafuwar cibiyar leken asiri domin yaki da ta'addanci, da kuma tsarin samun labarai a tsakanin sassa daban daban na kasar.

Sakamakon hali mai sarkakiya da tsanani da ake ciki kan yaki da ta'addanci, ana bukatar kafa wata doka ta musamman kan hakan, da kuma kyautata tsarin doka a wannan fanni.

Bugu da kari, sakamakon hadin gwiwar da kasar Sin ke da shi da kasashe da yankuna masu yawa kan yaki da ta'addanci, ya sa ya fi kyau a kara kyautata tsarin doka a wannan fanni, wanda zai taimaka wa kasar Sin wajen samun fifiko a cikin ayyukan hadin gwiwar kasa da kasa a wannan fanni.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China