in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe wani da ake zargi da dan ta'adda a birnin Mombasa
2014-11-09 16:32:32 cri
Wasu mahara da ba'a tantance su ba sun kashe wani mutum da ake zaton da dan ta'adda ne a ranar Asabar a Mombasa, birnin dake bakin teku na kasar Kenya dake fama da matsalar rashin tsaro. Kwamandan 'yan sandan birnin Mombasa, Geoffrey Mayek ya bayyana cewa Hassan Guti na daga cikin jerin sunayen da jami'an tsaro ke sa ido kansu tun da jimawa, an kashe da harsashe hudu wanda wasu mutane da ba'a tantance su a cikin mota suka harba kansa. Marigayin na cikin motarsa a yayin da mutanen suka hana motarsa wucewa kafin su kashe shi. Muna nan muna bincike kan dalilin wannan kisa in ji mista Mayek a gaban 'yan jarida. Haka kuma ya jaddada cewa Hassan Guti na tare da matarsa da kuma wata mace a yayin da motarsa ta sha ruwan harsashe ta wajen bangaren da yake tuki.

Mista Guti ya mutu a yayin da yake samun jinya a wani asibiti mai zaman kansa, a yayin da matarsa ta samu raununuka maras tsanani.

A cewar mista Mayek, ana zargin Guti da kasancewa daga cikin matasan dake cikin kungiyoyin ta'addanci a birnin Mombasa. Haka kuma a cewar wata majiyar 'yan sanda, Guti na daga cikin jerin sunayen da jami'an 'yan sanda ke sa ido wadanda kuma suke da hannun a cikin ayyukan ta'addanci da na munanan laifuffuka. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China