A lokacin tattaunawar, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta dauki bakuncin gudanar da taron, kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Yesui ya nuna cewa, tare da bunkasuwar fasahohin internet, kafar ya zama muhimmiyar hanyar yin mu'amala da aiwatar da ayyuka ga kungiyoyin ta'addaci, wadda ta kara kawo illa ga kasa da kasa.
Zhang Yesui ya yi bayanin cewa, kasar Sin kasa ce da take fama da ta'addanci ta hanyar internet. A shekarun baya, kungiyar Eastern Turkistan Islamic Movement ta maida hanyar internet a matsayin muhimmin dandali wajen gudanar da ayyukan ta'addanci, wadanda suka kawo barazana ga tsaron kasar Sin, kana suka kawo illa ga zaman lafiya da na karko a yankin. Don haka ya ce, kasar Sin ba za ta amince da duk irin aikin ta'addanci ba, kuma za ta hada gwiwa da sauran kasashe wajen yaki da ta'addanci.
Taken taron a wannan karo shi ne kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa wajen rigakafi da yaki da ta'addanci ta hanyar internet, inda mahalartar taron suka yi musayar fasahohi wajen daukar matakan tinkarar batun gudanar da ayyukan ta'addanci ta hanyar internet da kungiyoyi ko masu zaman kansu suke yi, da kuma tattauna kan yadda za a kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe daban daban da daga karfinsu wajen yaki da ta'addanci ta hanyar internet. (Zainab)