Ministan harkokin waje na kasar ta Bahrain Khaled al-Khalifa a jawabin da ya gabatar ya ce, kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS tana samun kudade ne ta hanyar wawushe bankuna da kuma mallakar rijiyoyin mai a sassan da ta mamaye. Ban da haka, wasu mutane masu zaman kansu da kuma kungiyoyi ma suna tallafawa kungiyar ta IS da kudade. Don haka, ministan ya yi kira ga kasa da kasa da su kafa wani tsari na tabbatar da cewa, an toshe dukkan kafofin shigowar kudi da ke shigowa hannun kungiyoyin 'yan ta'adda, tare kuma da hana kungiyoyin 'yan ta'adda gudanar da haramtattun harkokin ciniki da suka hada da fasa kwauri.
Wakilai daga kasashen Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin da kuma kasashen Larabawa da ma bankin duniya da asusun ba da lamuni na duniya sun halarci taron da aka yi a wannan rana.(Lubabatu)