A wannan rana an gudanar da cikakken zama na babban taron MDD karo na 69, inda aka tattauna batun yiwa kwamitin sulhu na MDD kwaskwarima. A jawabinsa Wang Min ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan shirin yiwa kwamitin sulhun kwaskwarima, a ganinta, ya kamata a yi kwaskwarimar bisa manufar kara samar da wakilci da ikon fada aji ga kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka, sannan a kara shigar da yawan kasashe matsakaita da kanana mambobin MDD cikin kwamitin sulhu domin bada shawara da taka muhimmiyar rawa, a kokarin kiyaye manufofi da ka'idojin kundin tsarin MDD da kuma babbar ka'idar kula da dangantakar dake tsakanin kasa da kasa.
Ban da wannan kuma, Wang Min ya bayyana cewa, yayin da ake kokarin yin kwaskwarimar, akwai bukatar kasashe mambobin MDD su yi shawarwari da yin la'akari da juna, musamman kula da muradun kasashe matsakaita da kanana don neman cimma matsaya guda. (Zainab)